Yanda zaka dawo da account dinka Gmail, facebook ko WhatsApp

 

Yanda zaka dawo da account dinka Gmail, facebook ko WhatsApp 


Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.


Wannan wani Application ne


Sunansa Google Authenticator, wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, sama da mutum miliyan dari ne 100M suke amfani dashi, kaima kar ka bari a baka labari.


Mene amfanin wannan Application din?


Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin kare kanka daga masu satar Account, kuma ko wani kalar account tun daga kan Facebook, Gmail, Instagram da sauransu, wannan Application din zai hana a kwace maka su.


Google Authenticator zai kara baka damar dawo da account dinka wanda ka manta bayanansa misali idan ka manta password ko kuma lambar waya, to wannan zai taimaka maka gurin dawo da account din. Domin samun cikakken bayani akan wannan Application din ka bibiyi shafinmu na YouTube ko facebook mai suna mubarakeey zaka samu cikakken bayani. 


Idan kana san downloading dinsa 


Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan




Yanda zakayi downloading din wannan babban Application 


Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.


Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .


Bayan ka dakko shi, kai tsaye kana shiga zai nemi ka bashi ishashen iko a wayarka domin ya fara aiki, da zarar ka bashi dama shikkenan zaka fara amfani da shi.


Nasiha


Ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.


Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,

Wassalamu Alaikum

Mungode.

Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-