Ya kamata ku gaggauta sanin wadannan Applications din
Assalamu alaikum warahmatullah uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wasu manyan Applications masu matukar amfani wanda nasan zasu taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Application na farko ( Mobile secret Codes )
Sunansa Mobile secret codes, wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, sama da mutum dubu dari ne 100k suke amfani dashi, kaima kar ka bari a baka labari.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin sanin sirruka boyayyu na wayar hannnu, kuma ko wata kalar Waya ce da kai zaka samu sirruka da dabaru wanda zasu taimaka maka gurin kara sanin wayar.
Sannan zaka samu codes masu Muhimmanci, kamar code din ganin bayanan waya, ko code din rufe lambar waya da sauransu. Sannan zaka ga cikakken bayani akan wayar da kake amfani da ita, version dinta da model da sauransu.
Idan kana san downloading dinsa
Application na biyu ( ChatGpt )
Sunansa chatgpt, wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, sama da mutum miliyan biyar ne 5M suke amfani dashi, kaima kar ka bari a baka labari.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin yin bincike da kuma samun abinda kake bukata cikin kanciyar hankali. Nasan ma bakwa bukatar karin bayani akan wannan, domin kowa ya sansa.
ChatGpt da basuda Android Application sai dai kayi amfani da browser amma yanzu zaka iya amfani da shi A wayar ka ta hannu.
Idan kana san downloading dinsa
Application na Uku (Incoming call lock)
Sunan Application din Incoming call lock, wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, sama da mutum miliyan biyar ne 5M suke amfani dashi, kaima kar ka bari a baka labari.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din zai taimaka maka sosai gurin hana mutane daga wayarka idan an kiraka. Wasu mutanen idan wayarka tana hannunsu daga ankira ka zasu daga, ba tare da jin kunya ba.
Idan ka saita wannan Application din a wayarka shikkenan ba wanda ya isa ya daga wayarka dole sai ya san code din daga wayar, idan baka fadawa kowa ba ka ga kai kadai ne zaka iya dagawa.
Idan kana san downloading dinsa
Application na biyu ( Charge Meter )
Sunansa Charge Meter, wannan Application din mutane da yawa sun dauko shi domin yin amfani dashi, sama da mutum dubu dari ne 100k suke amfani dashi, kaima kar ka bari a baka labari.
Mene amfanin wannan Application din?
Wannan Application din zai magance maka matsalar battery, domin zai sanar da kai komai akan battery na yawarka, zaka san halin da yake ciki.
Ya kamata kuyi downloading dinsa domin zai taimaka sosai.
Idan kana san downloading dinsa
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Bayan ka dakko shi, kai tsaye kana shiga zai nemi ka bashi ishashen iko a wayarka domin ya fara aiki, da zarar ka bashi dama shikkenan zaka fara amfani da shi.
Nasiha
Ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.