ARTIFICIAL INTELIGENCE

 ARTIFICIAL INTELIGENCE



Assalamu alaikum, yan uwa barkanmu da wannan lokaci dafatan kuna nan lafiya, a wannan darasin zamuyi dubane a inda duniya tasa a gaba a bangaren Technology ma'ana (Artificial Intelligent). zanyi mana bayani akan wasu guda uku duk da suna da matukar yawa.

STOCKIMG.AI

Wannan wani website ne me abin mamaki, domin acikinsa zaka iya kirkirar duk kalar photon da kake bukata,misali duk abinda yazo ranka. zaka iya sakashi ya zana maka gari, ko kauye, ko birni, kuma zaka iya rubuta masa cikakkiyar gumla domin ya hada maka photonta, misali kace 'hadamin photon africa a shekarar 1677' shi kuma zaiyi amfani da artificial intelligent domin  zana maka. na tabbata da wannan website din zai burge mutane da dama.

wannan shine link dinsa

Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


ADOBE PODCAST


Wannan ya shafi duk wanda yake mu'amala da sauti. idan kana video a tiktok ko youtube ko facebook kuma kana samun matsalar sauti to wannan AI din zaiyi maka maganin wannan matsalar, zai tace maka sauti kaji kamar a studio kayi videon, kuma zaka iya amfani dashi free. ina recommending din wannan idan kanaso ka gwada guda daya.

wannan shine link dinsa

Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan


BARD

Wannan yafito daga kamfanin Google, dan haka babbar harka ce acikinsa. Amfaninsa shine ya baka amsar duk abinda ka tambaye shi, zaka iya amfani dashi domin rubuta littafi ko koyan kasuwanci ko yin Assignment ko project.

Ni kaina yana daya daga cikin abubuwan da nake amfana dasu, domin zai taiamaka maka matuka a gurin koyon kowani yare. ina fatan zaka gwada shi.

wannan shine link dinsa

Danna Nan

Danna Nan

Danna Nan

Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.

Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.

Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.

Mungode.

Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-