Muhimman Technology guda 5
Assalamu alaikum warahmatullah, Barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin. A yau zamuyi muku bayani ne akan wasu manyan Technology guda 5 wanda na tabbata da mutane da yawa zasuji dadin amfani dasu a rayuwarsu ta yau da gobe.
Kowanne acikin wadannan Technology mun ajiye muku video wanda zakuje ku kalla domin sanin komai akansa.
Technology na farko
Wayoyin Tesla (Tesla phones)
Wadannan wasu wayoyine wanda ake sa ran zasu fito bada jimawa ba, kuma zasu zo da abubuwa masu matukar amfani, kamar chaji da hasken rana, Unlimited Network da dade sauransu.
Domin kallon cikakken video akan Tesla phones
Technology na biyu
Gilas din Apple (Apple Glasses)
A takaice glass din Apple glass ne wanda zaka na amfani dashi domin sarrafa wayarka ba tare da ka taba ta ba, zaka iya daga kira ko duba labarai da dai sauransu, kuma a jikinsa akwai camera guda biyu wanda zasuna daukar duk abinda kakeyi, Wannan Glasses din yana da matukar burgewa.
Domin kallon cikakken video akan Apple Glasses
Technology na uku
Meta vase (Duniyar Na'ura)
Meta vase wani project ne wanda kamfanin Meta (facebook) suka saka a gaba a yanzu, Domin kirkirar sabuwar duniya wanda mutum zai kasance a cikinta ba tare da damuwa ba, misali idan kana gida kai kade, zaka iya amfani da Meta vase domin ka daukewa kanka kewa, domin zaka iya yin game da mutane wanda baka ganinsu.
Domin kallon cikakken video akan Meta vase
Technology na hudu
Mota mai amfani da lantarki (Electric Car)
A shekarun baya kamfanoni suka fara fitar da motoci masu amfani da wutar lantarki, kamar kamfanin Tesla da sauransu. Motoci masu amfani da wuta suna da abin burgewa sosai, domin zasuna iya tuka kansu, kuma zasuna taimakawa mutum a yayin tuki, sannan baka da matsalar karewar fetir ko kuma ya kara tsada.
Domin kallon cikakken video akan Electric Cars
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yan uwa a nan darasin namu zai dasa aya, idan wannan bayanin ya burgeku kada ku manta kuyi sharing domin yan uwa da bokanan arzuki su amfana.
Mungode.