yanda zaka gane lokacin daukar kowane hoto
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan Timesnap, hakika wannan App din ya kamata a ce muna aiki dashi a koda yaushe duba da yanda zamani yake canzawa duniya take kara samun ci gaba, komai yanzu yana bukatar hujja, to da wannan App din zaka iya yin duk wannan abubuwan da muka lissafo a sama
Menene babban aikin wannan App din?
A wasu lokutan zakaga mutum yanasan ya dauki hoton wani abun domin ya nunawa wani ogansa ko kuma wata ma'aikata yanda abun ze zama hujja ... to wannan App din ze taimaka maka wajan daukar maka lokacin da ka dau hoton da kwanan watan a gefen hoto, abun yanada matukar kyau tare da burgewa a don haka idan ka dauko wannan App din zakaga sama da abinda muka bayyana a cikinsa.
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.