Yanda zaka kirkiri kowani kalar Application a wayarka
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a mu'amala da wayoyinku.
Wannan wani Application ne?
sunan wannan App din Clone App, wannan Application ne na kirkirar sabon Application, sannan wannan App din saukinsa da yake dashi da rashin nauyinsa tare da ingancinsa yasaka muka kawo muku shi domin jin dadinku.
Clone App, Application ne wanda zai baka damar ka kirkiri duk Application din da kake so, misali whatsapp, facebook, Instagram da sauransu. Duk zaka iya kirkirar irinsu a wayarka cikin sauki da jindadi. Kuma wannan Application din bashi da nauyi kuma bashi da wahalar gane wa.
Adan haka wannan App din ya zo maka da dukkan wannan
damar makin kawai kai aikink a ka shiga cikinsa don koyon
yanda ake amfani dashi cikin sauki
Idan kana san downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
wasalam, mun gode.