Application din da zaka dauki bayanan kiran waya.
Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, ayau zamuyi muku bayani ne akan wani babban Application wanda zai makukar burge ku.
Menene amfanin wannan App din?
Da farko wannan App din halastacce ne domin kuwa an
sauke shin a wajan dauko app na Google playstore
Hakika a zamanin yanzu duniya tana ta samun cigaba kala
dabam dabam, ta yanda zakaga amfanin sayen manyan
wayoyin da muke ya kamata ace muna morar su ta wajen
ire iren cigaban da duniya take samu.
Awasu lokutan akan kiramu a waya ko kuma muma mu
kira, kaga munyi magana me muhimmancin da be kamata
ace ta tafi haka ba ko kuma mun manta ko kuma mukanso
mu kafawa wasu hujja da musa maganar da kukai a waya
kai harma idan munasan bibiyar wace waya yaranmu suke
ko kuma matanmu da sauransu.
To fa muna iya amfani da wannan App din domin biya maka bukatun duk abinda muka lissafa a baya kamar
haka.
Wanda ya hada da adana dukkan kiraye kirayen damukai
sannan yabaka dama ka tura su izuwa ko ina, sannan
zaka iya Edit din wayar da kukai domin ka yanke wasu
abubuwan da bakasan kaji ko kuma wani yaji.
Wannan Application din yana da abubuwa da dama
zaka iya dubawa idan ka sauke shi wato akan wayarka.
Ina tinatar daku kuyi amfani da wannan Application din ta hanyar da ta dace bai kamata wani yayi amfani dashi domin yaci mutumci wani ko wata ba
Na tabbata da inka dakko wannan Application din zakaji dadinsa sosai.
Domin downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
wasalam alaikum.
Na gode.