Yanda zaka dauki hoton komai da wannan app din( Selection)
A yau mun zo muku da wani Application wanda ze baka dama kai screenshort ta hanyar kwarewa ba kamar yadda aka saba ba a baya.
Assalamu alaikum warahmatullah en uwa barkan mu da sake saduwa daku a wannan darasi da muke kawomuku wani application me matukar muhimmanchi
Kamar yadda yake a wasu lokuta da dama idan muna browsing ko kuma danna wayarmu mukan hadu da wani abu wanda mukesan daukan hotonsa,domin nunawa abokanmu ko kuma sakawa a story namu na flatform. Sedai a wasu lokutan mukan samu cikas wani rubutu ya shiga ko kuma wani hoto ya shigo abunda mukeso mu dauka, ta hakane zakaga muna ta faman yaya zamu cire wannan abun. Hakan yana haifara mana da matsalar mubarshi ko kuma semunyi amfani da wani App din
domin goge wannan wajan da bama so.
A adon haka mukazo muku da wannan app din me suna Selection, domin ya taimaka muku wajan Screen short din ko menene.. tare da kayyade inda kakeson dauka kai tsaye, ba tare da ka yanke can ko kuma ka goge nan ba.
A dan haka munajin sunan wannan App din zamu gane cewa ze mana dukkan wani aiki da baya yuwawa sai a manyan wayoyi.
Sauki da rashin nauyin wannan App din na daya daga abunda yasa mukazo dashi domin jin dadinku
Don ganin yadda ake saita wannan abun mamakin kawai kaje ka dauko.
Munyi cikakken video akan wannan Application din a channel dinmu ta mubarakeey tv
Yanda xaka yi download din wannan app
Idan bayani da tsarin wannan app sun burgeka kaga ya kamata ka dauko shi, to hanyar tana da matukar sauki zaka yo kasa za kaga kalama da alamar ruwan omo an rubuta download ka danna ta zata kaika gun download din app din
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.
Wannan shine karshen darasin idan ya burgeku kada ku manta da shere da like mungode