Sirrukan bluetooth wanda mutane basu sansu ba
Assalamu alaikum warahmatullah, yan uwa barkanmu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin, a yau zamuyi bayani ne akan wani babban Application mai matukar amfani wanda nasan zai taimaka muku sosai a wayoyinku na hannu.
Wannan wani Application ne
Sunansa (Bluetooth audio widget) wannan Application din mutane sama da miliyan daya ne sukayi downloading dinsa kuma bashi da nauyi kwata-kwata.
Mene amfanin wannan Application din?
Amfaninsa shine zai baka damar ka sarrafa bluetooth din ka duk yadda kaso.
Kamar yadda kuka sani muna amfani da bluetooth sosai a wayoyinmu na hannu , dashi muke amfani domin ture-ture, dashi muke amfani domin jin sauti a abun jin sauti, dan haka bluetooth yana daya daga cikin abubuwan da muke amfani da su sosai.
A wannan Application din zaka samu damar yin amfani da bluetooth a saukake, misali idan kana ture-ture a wayarka zaka ga kana da sunaye da yawa a cikinsa, to wannan Application din baka damar ka hada musu widget a wayarka ta yadda kana bukata kai tsaye kana danna shi zai hadu. Nasan ba lalle bane ka fahimci abinda nake nufi dari bisa dari ba, amma idan ka kalli wannan video zaka fahimci komai da yardar Allah domin nasan tabbas wannan Application din zai burge ka.
Domin downloading dinsa
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Yanda zakayi downloading din wannan babban Application
Kai tsaye zaka danna gurin da nace maka ka danna ma'ana (Danna Nan), bayan ka danna kai tsaye zai kaika play store , A nanne zaka ga komai na wannan Application din : Adadun mutanen da sukayi downloads dinsa da Nauyinsa da kuma dukkan bayanasa.
Kai tsaye zaka danna Install shikken nan zaka fara Amfani da shi , na tabbata da zakaji dadin wannan Application .
Ina fatan zakuji dadin wannan Application din,
Wassalamu Alaikum
Mungode.