Yanda zaka iya crop din hotonka a whatsapp ba tare da ya tabu bah
Assalamu alaikum warahmatullah en uwa barkan mu da sake saduwa daku a wani darasi me matukar muhimmanci akan wani application daze temaka mana sosai wajen ganin mun dora hoton daya dace a whatsapp dinmu
Wanne application neh
Application dinmu na yau sunansa whatscrop application neh daya shahara sosai a bangaren yanke hoton dorawa a profile na whatsapp idan ka shiga google play za kaga jamaa da yawa sun daukoshi saboda amfanin sa kuma yana da matukar sauki
Ya yaje aiki
Kamar yanda muka sani ne cewa idan muka yi tafiya ko kuma mu kaje wani biki muna shaawar muyi kala kalan hotuna wasu a kwance wasu a tsaye bayan mun kammala za kaga muna shaawan mu dan dorasu a profile dinmu na whatsapp domin mu nuna jin dadinmu sede matsalan shi whatsapp baya karbar wannan size din
To a nan amfanin wannan application din ze bayyana saboda shi amfanin sa ze seta maka hotonka ya zama dede da size din whatsapp ba tare daya yanke komai a jikinsa ba .
Amfaninsa
Wannan application ze saukaka maka sosai wajan dora profile me kyau ta hanyar data dace
Sannan ze tamaka wajan ragemaka hanya ta se kayi edit din hoto kafin ka dora
Sannan ze baka dama kana samun size din da kakeso a profile dinka na whatsapp
Yanda za kayi download dinsa
Kamar yanda kuke gani hanyar download din application dinnan bata da wahala ko kadan hanyace me sauki sosai kawai abin da zaka yi zaka danna wannan kalmar ta download dake kasa kai tsaye ze maka download
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.
Wannan shine karshen darasin mungode wassalamu alaikum