Kwanannan company whatsapp zasu cure wasu wayoyin daga jerin masu Amfani da manhajar tasu
WhatsApp Blog sun Samar da cewa mashahurin Application dinsu na sada zamunta ze dena aiki a cikin wasu wayoyi masu yawa a cikin shekarar nan wayoyin da ze dena aiki a cikinsu sune wayoyin da suke aiki da tsohon operation system daga kan android har iPhone sannan kamfanin ya fadi sunan wayoyin da whatsapp ze dena aiki a kansu.
A wacce waya whatsapp ze dena aiki
Whatsapp ze dena aikine a wayoyin android daga kan 4.0.3 zuwa kasa da kuma wayoyin iphone da suke aiki da tsarin ios 9 zuwa kasa saboda whatsapp yayi bayani kan cewa ya kamata mutum ya mallaki wayoyin zamani saboda ya morewa dukka tsarukan da application din zezo dasu
Game da wayar iphone
Kamfanin whatsapp sun bada sanarwa game da wanda suke amfani da wayar iphone ya kamata ayi update din wayoyin iphone4, iphone5, iphone5s, iphone6, iphone6s zuwa update na sama da 9.
Wasu daga wayoyin da zasu dena daukar whatsapp
Kamfanin ya bada misali da kadan daga irin wayoyin android da zasu dena aiki da manhajar tasa masu Android 4.0.3 misalin lg optimus, htc desire 9, motorola droid razr 9, samsung s2.
Idan kana so ka gano version din wayarka
Zaka shiga setting>about>version anan za kaga wanne version kake dashi .
Kuma ya kamata yan uwa mu karfafa binkice domin akwai abubuwa na zamani wanda ya kamata ace kowannenmu ya sansu, domin a kullum duniya tana kara samun cigaba ne, ta hakane zamu gyara kasuwancin mu, kuma mu samu sababbin hanyoyin samun kudi a Internet, Muna fatan mutanenmu zasu farga daga baccin da mukeyi.
Sannan Yawancin wadanda Applications din zaku iya samunsu a playstore, muna fatan idan kana da wani karin bayani ko kuma tambaya, zaka iya yinta a kasan wannan post din, agurin comment.
Daga karshe muna fatan zakayi sharing din wannan posting din domin yan uwa suma su gani su amfana.