Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi asarar dala miliyan 900 a hada-hadar hannun jari ta Najeriya
Assalamu Alaikum warahmatullah. Yan uwa muna yi muku fatan Alkhairi.
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya yi asarar dala miliyan 900 wanda tayi ya kusa kai kudin Nigeria Naira Trillian 35 a hada-hadar hannun jari ta Najeriya, kamar yadda jaridar kasuwanci ta Bloomberg ta bayyana.
Jaridar Bloomberg wadda ke bayar da rahoto kan mutum 500 wadanda suka fi kowa kudi a duniya, ta nuna kudin Dangote sun ragu daga biliyan $18.4 a ranar Alhamis zuwa biliyan 17.5 a ranar Juma'a, wanda hakan ya sa ya sauko daga mutum na 106 zuwa na 114 a jerin masu kudin duniya, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
A watan Disambar bara ne jumullar kudin Dangote ya kai dala biliyan 17.8 daga dala biliyan 15.5.
Dangoten ya sake samun karin dala miliyan 600 a farkon makon Janairun 2021, sai dai ya yi asarar duka kudin a Juma'ar da ta gabata.
Duk da haka Dangote shi ne wanda ya fi kowa kudi a nahiyar Afrika, haka kuma shi ne ya fi kowane bakar fata kudi a duniya.
RA'AYUNKU
Shin a ra'ayunku menene ya jawo masa wannan Asarar?