Sabin abubuwa a whatsapp 2021

 


Babban kamfanin sada Zumunta na duniya wato Facebook yana kokarin karawa daya daga cikin kayayyakinsa wato sabin canje-canje a cikin wannan shekara da muka shiga ta 2021 saboda karamasa kyau da kuma saukin Amfani.

Abu na Farko

Abu na farko da kamfanin suke kokarin karawa whatsapp shine multi-use maana zasu meda  account daya yana aiki a wayoyi daban daban kamar messenger.

Yanzu Idan kana whatsapp da lambarka guda daya amma wayoyinka Sunkai kamar guda dukkan su zaka iya sakamusu whatsapp dinka guda kuma kana amfani dashi a tare cikin sauki.

Abu na biyu

Abu na biyu da suke so su karawa whatsapp shine goge message da kansa wanda kaso kamar yanda kuka gani a karahen 2020 whatsapp ya fara kawo tsarin sakon da zena gogewa bayan kwana 7 to kamfanin yana so ya karawa wannan tsari karfi ta yanda zena iya gogewa a mintunan daka tura sakon ko aka turomaka.

Abu na uku

Abu na uku shine facelock kamar yanda muka sani a  wasu update na whatsapp da suka gabata ya kirkiro tsarin kulle whatsapp ko kuma sakamasa tsaro ta hanyar pingerprint ta yanda duk wanda ze shiga whatsapp dinka seya saka dan yatsa ze bude to babbar matsalar wannan tsari dole se wayoyi masu amfani da dan yatsa ne sukeyi shiyasa yanzu whaysapp ze kawo hanyar kulle whatsapp ta hanyar camera selfie wanda kowacce waya tana da ita.

Abu na hudu

Abu na hutu shine break ; wannan tsari ba sabo bane game da duniya saboda mungansu a wasu chat da suke gasa da whatsapp kamar su telegram maana zaka iya kulle account dinka na dan lokaci idan mutane sun nema ba zasu sameka ba ba zasu iya turomaka sakoba har se lokacin da gama hutunka ka dawo whatsapp sannan babu abin daze goge a bayanan ka na whatsapp Yanzu haka kamfani suna kan ci gaba da aiki.

Abu na biyar

Abu na biyar shine shine yaduwar whatsapp payment a duniya kamar yanda muka sani a kusan karshen shekarar 2020 kamfanin whatsapp suka kirkiro tsarin hanyar biyan kudi ta cikin whatsapp don daukaka hanyar kasuwanci to amma se suka ki su sakarwa duniya wannan tsarin suka barshi a wasu en kasashe kadan daga cikin su akwai irin su brazil don su gwada suga yanda ze kasance ,Bayan dogon gwaji yana daga abin da ake tinani kamfanin zasu sakarwa duniya shi a cikin wannan shekara .

Tushen labarin : Dannan nan

Wannan sune kadan daga canje canjen da ake sa ran zasu zo a whatsapp wannene a cikinsu kake shaawar kaga ya tabbata ku fadamana raayinku agun comment .


Comments



Font Size
+
16
-
lines height
+
2
-