Abubuwan da ya kamata kowa ya sani game da Alqur'ani
Assalamu Alaikum warahmatullah yan uwa barka da warhaka sannumu da sake saduwa daku a wannan sabon darasin mai muhimmanci.
A Wannan darasin zamuyi bayani ne akan littafin da yafi kowanne littafi a duniya wato Alqur'ani (Babban Kundi). Kamar yadda muka saba a kullum muna kokari muga munkawo muku duk wasu abubuwan da zasu taimaka muku gurin ayyukan ku na yau da gobe.
Dan haka muka kawo muku wasu manyan Applications wanda zasu taimaka muku gurin karanta Alqur'ani mai girma kuma da fahimtar shi.
Kadaure kayi Install din qurani a wayarka.
Zamu fara daga na uku zuwa na 1
Application na uku
Alqur'ani warsh rubutun hannu
Wannan qur'anin rubutun hannune, kuma yasamu kyakyawan aiki wanda yankunshi dukkan abunda zai sa shi ya zama mai dadin amfani kuma shine na farko bukun hannu a duniya wanda ke kunshe da sigan rubutu na kira'an warshu. Sannan akwai kira'an alaramma malam yahuza bauchi a wasu surorin saboda kananan yara, (Allhmdllh).
Na tabbatar da zai burge ku.
Domin download dinsa
Alqur'ani warsh
Alqur'ani Warsh, kur'ani ne na kyauta wanda yake amfani da riwaya Warsh 'an Nafi' Yawancin fasalluka suna haɓaka ƙwarewa yayin karatun ko haddar Alƙur'ani. Wannan aikace-aikacen yana amfani da shi, ba kamar sauran aikace-aikacen ba, rubutu na ainihi maimakon hotuna, wanda ke inganta karantawa sosai a kowane nau'in allo. Wadannan fasali suna nan a cikin Warsh Quran: - Nemo surah bisa taken - Nuna taken suwar cikin larabci - Yi wa aya alama - Yanayin dare - Tsallaka zuwa Hizb ko Thoemoen ta amfani da shafin Juz - Sanya tsakanin hanyoyin nunawa (Salon Jerin / Salo na gargajiya) - Sake fasalin matanin Alqurani zuwa girman da ake so - Tsallaka zuwa aya takamaiman - Karatun Audio tare da nuna goyan baya - Zaɓuɓɓukan maimaita ci gaba.
Domin download dinsa danna
Alqur'ani Hafsu
Wannan shine Application na qurani wanda banta ba ganin irinsa ba. Tabbas wannan app zaka karu dashi sosai.
Abubuwan da yake dasu
1. Karatun malamai masu yawan gaske
2. Tarjamar kalma zuwa Kalma( ma'ana daga larabci zuwa Hausa)
3. Damar mai-maita duk ayar da kake so ko surah
4. Zaka iya karantashi cikin dare ba tare da ya tsutar da idan ka ba (Dark mode)
Da sauransu
Domin yin Download dinsa danna
Ku fada mana Raayinku akan wannan darasin.
Wassalamu Alaikum
Mungode.