Abinda yasa Telegram yafi whatsapp
Bayan matsalar da mutane suka samu tsakaninsu da Whatsapp hakan yasa mutene keta kumawa Telegram domin cikagaba da harkokinsu na yau da gobe. Dan haka yau muka kawo muku kadan daka sirrukan Telegram.
Zaka iya goge sako
A Telegram in ka tura sako zaka iya goge shi batate da wanda ka turawa ba ya gani, kuma koda yayi amfani da wasu Application din da suke saving din Notification. Amma whatsapp indai ka tura to wanda ka turawa zai iya gani koda ka goge.
Zaka iya bode group da mutane 200, 000
A Telegram zaka iya bude group wanda zai iya daukar sama da mutum dubu dari biyu 200,000, amma whatsapp yana daukar mutum 200 kawai
Tura video ko Audio
A Telegram zaka iya tura abu mai nauyin 2GB, Amma whatsapp sai dai 100MB.
Ina kokarin nayo muku shi a Table ta yadda zakufi fahimta sosai.